Isa ga babban shafi

India ta kalubalanci Canada kan ta kawo shaidar kisan Hardeep Singh

Gwamnatin India ta kalubalanci Canada kan ta kawo duk wata shaida, wadda zata tabbatar da zargin da take yi mata na hannu a kisan da gwagwarmayar samar da kasar ‘yan Kabilar Sikh ta India.

Ministan harkokin wajen India Subrahmanyam Jaishankar
Ministan harkokin wajen India Subrahmanyam Jaishankar © Bay Ismoyo / AP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da alaka ke kara tsami a tsakanin kasashen biyu mambobin kungiyar G20.

Ministan harkokin wajen India Subrahmanyam Jaishankar, wanda ke yiwa taron majalisar dinkin duniya jawabi, ya ce India ba zata dauki duk wani salo na katsalandan ko nuna isa daga wata kasa a harkokin ta na cikin gida ba.

Tun bayan kisan Hardeep Singh Nijjar wanda Canada ta zargi India da kitsawa ne kuma alaka ta fara tsami a kasashen biyu, inda Canada ke ganin ba zata lamunci India ta kitsa aikin ta’addanci a kasar ta ba kasancewar an kashe Mr Hardeep ne a Canada, yayin da ita kuma India ta musanta zargin sannan ta ke ganin ya kamata ta dauki mataki kan Canada wadda ta dade tana yi mata katsalandan.

Tuni dai kasashen biyu suka janye jakadun su da kuma rage yawan ma’aikata a Ofisoshin jakadancin su.

Kawo yanzu jami’an tsaro a Canada sun kama mutane 8 da ake zargi da hannu a kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.