Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 25 yayin wani taron addini a Pakistan
Rahotanni daga Pakistan na cewa akalla mutane 25 sun mutu a harin kunar bakin wake da aka kai yayin wani taron addini yau Juma’a a lardin Balochistan na kasar.
Wallafawa ranar:
Karamin ministan lardin na Balochistan Zubair Jamali ya tabbatar da cewa mutane 25 sun mutu nan ta ke sai kuma wasu fiye da 80 da suka jikkata.
A cewar minista Jamali cikin jerin wadanda suka jikkata har da wasu 20 da ke cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sanya fargabar yiwuwar karuwar mamata a harin na yau.
Rahotanni sun bayyana cewa dan kunar bakin waken ya yi damarar bom tare da shiga cikin dandazon mutanen da ke halartar taron addinin na Yau juma’a.
Ko a watan Yulin da ya gabata, sai da wani harin ta’addanci ya hallaka sojojin Pakistan 12 a Lardin na Bolichistan kari kan kisan jami’an tsaro 9 cikin watan Maris duk dai a yankin mai fama da matsalar tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu