Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu sanadin girgizar kasar Afghanistan ya zarce 2,000

Adadin wadanda girgizar kasa ta hallaka a Afghanistan ya zarce dubu 2, yayin da ake ci gaba da neman masu sauran numfashi a karkashin baraguzan gine-ginen da suka fadi.

Kawo yanzu dai babu cikakkun alkaluma kan yawan mutanen da girgizar kasar ta raba da muhallan su
Kawo yanzu dai babu cikakkun alkaluma kan yawan mutanen da girgizar kasar ta raba da muhallan su © ALI KHARA/REUTERS
Talla

Girgizar kasar mai karfin maki 6.3 wadda ta faru bayan jerin motsin kasa sau 8 ta lalata kauyuka da dama a yankin Herat, inda lamarin ya fi kamari yayin da gine-gine suka zama kasa bayan da suka fadi kan mutane.

Mai Magana da yawun gwamnatrin kasar Bilal Karimi ya ce abin takaici ne yadda adadin mamatan ke kara yawa cikin sauri, yana mai cewa barnar da girgizar kasar ta yi a bayyane take.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da safiyar yau, Bilali ya ce har yanzu gwamnati na jiran ganin adadi na karshe kan yawan mutanen da girgizar kasar zata yi ajalin su kafin shirin fara gyara ko kuma tallafawa wadanda lamarin ya shafa.

Hukumar lafiya ta duniya ta fitar da alkalman gidaje fiye da 600 da suka ruguje, abinda ya raba  mutane sama da 4,200 da muhallansu a kauyuka 12 na lardin Herat.

Bashir Ahmad guda daga cikin wadanda lamarin ya shafa, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa a girgiza daya tak, baki daya gidajen da ke kewaye da unguwar su suka zube.

Bashir yace gine-ginen da suka zube sun binne wadanda ke cikin su, inda ya ce har yanzu babu labarin ko da mutum guda daga cikin iyalan gidan sa da gini ya fada musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.