Isa ga babban shafi

Tsohon Fira Ministan Pakistan Nawaz Sharif da ya yi hijira ya koma gida

Nawaz Sharif, wanda ya  yi firaa minister a kasar Pakisatn har karo 3, ya kawo karshen hijirar  shekaru 4  da yayi  ta kashin kansa a ranar Asabar, inda ya koma gida, ya kuma kaddamar da dawowar sa  fagen ssiyasar kasar a wani gangami da ya samu halartar dubban magoya bayansa, gabanin babban  zaben kasar da zai gudana a  shekara  mai zuwa. 

Tsohon Fira Ministan Pakistan Nawaz Sharif yana sanya hannu a takarda bayan saukarsa kasarsa a filin jirgin saman kasar ranar 21ga watan Oktoba, 2023.
Tsohon Fira Ministan Pakistan Nawaz Sharif yana sanya hannu a takarda bayan saukarsa kasarsa a filin jirgin saman kasar ranar 21ga watan Oktoba, 2023. © AFP
Talla

An yi wasa da tirtsitsin wuta don nuna farin cikin dawowar tasa a gangamin da aka yi  a birin Lahore, inda aka kawata tituna da tutocin jam’iyyarsa masu launukan kore da ruwan daurawa. 

Pakistan na fuskantar matsalolin da suka hada da na tsaro, tattallin arziki da siyasa, gabanin babban zaben kasar da aka matsar da shi zuwa watan Janairun shekarar 2024, a yayin da babban abokin hamayyar Sharif, Imran Khan ya ke a garkame  a  gidan yari. 

A yayin gangamin, jawabin Sharif ya ta’allaka ne a kan bukatar dakile matsalar hauhawar farashin kayayyaki da hadin kan kasa, akasin yadda abokin hamayyarsa Khan, wanda ke caccakar hafsoshin sojin kasar da bangaren shari’a.

Sharif, wanda ya kafa jam’iyyar Pakistan Muslim  League-Nawaz (PML-N)  yana zaman gidan yari ne sakamakon samun sa da laifin Rashawa a lokacin da ya bar kasar a shekarar 2018 don neman magani a Birtaniya saboda lalurar rashin lafiya da ta same shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.