Isa ga babban shafi

Kotu ta fara tuhumar Imran Khan da laifin cin amanar kasa

Wata kotu a Pakistan ta fara tuhumar tsohon prime ministan kasar Imran Khan da laifin cin amanar kasa da kuma fitar da sirrikan da basu dace ba.

Tsohon Prime ministan Pakistan Imran Khan
Tsohon Prime ministan Pakistan Imran Khan AP - K.M. Chaudary
Talla

Cikin wannan tuhuma da ake yi masa har da wasu karin laifukan da aka zarge shi da aikatawa a 2022 lokacin da aka cire shi.

Shah Khawar mai gabatar da kara na gwamnatin kasar ya shaidawa manema labarai cewa bayan fadada bincike kan laifin da ake zargin Mr Khan da aikatawa, an gano yadda ya rika yiwa kasar zagon kasa ta hanyar bankada wasu muhimman sirrika.

Ana dai tuhumar Khan kan wannan zargi tare da mataimakin sa Shah Mahmood Qureshi, wadanda dukannin su ke daure a gidan yarin Adiala da ke wajen birnin Islamabad.

Tuni mai magana da yawun jam’iyyar Mr Khan Tehreek-e Insaf ya ce wannan tuhuma bata da bambanci da wasan yara, kasancewar an yi amfani da dokokin da turawa mulkin mallaka suka samar tun kasar na karkashin su, wajen shigar da karar, don haka dole zasu kalubalance ta.

Ana dai zargin Mr Khan wanda ya jagoranci kasar daga 2018 zuwa 2022 da fitar da wata takarda da ke nuna yadda  Amurka ta yi amfani da karfin iko wajen fitar da shi daga Ofis, kawai don biyan bukatar kanta, abinda tuni Isamabad din ta musanta, tana mai cewa Mr. Khan ya kirkiro wannan takarda ne kawai saboda wata boyayyiyar manufa tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.