Isa ga babban shafi

Zabtarewar kasa 1,000 aka samu yayin girgizar kasar Japan

Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutanen da baraguzan gine-gine suka danne a sakamakon gurgizar kasar Japan wadda kawo yanzu ta kashe mutane 126.

Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutanen da gine-gine suka danne
Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutanen da gine-gine suka danne AP - Pradeep Kumar
Talla

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyar da faruwar girgizar kasar.

Girgizar kasar mai karfi maki 7.5 ta fara aukuwa ne a yankin Ishikawa, kuma har yanzu akwai mutane 210 da ba’a san inda suke ba.

Bayanai sun ce a ranar da girgizar kasar ta faru sai da kasa ta zabtare sama da sau dubu 1 a sassan kasar.

A wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ce rashin ingancin yanayi da tsananin sanyi na zama tazgaro ga aikin ceto.

Ko da yake jawabi jagoran hukumar bada agajin gaggawa ta kasar, yace a yanzu masu aikin ceto sun daina neman masu rai, abinda akeyi yanzu shine neman gawargwakin wadanda gine-gine suka danne.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa gine-gine fiye da dubu 3 ne suka ruhse a sanadin girgizar kasar.

Japan na cikin kasashen duniya da ake yawan samun rahoton girgizar kasa da ke sanadin mutane da dama a kowanne lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.