Daga Jigawa nake zuwa Kaduna bara saboda mijina ya hana ni abinci
Wallafawa ranar:
Hafsat ta shaida wa RFI Hausa cewa, tana zuwa jihar Kaduna ne daga Jigawa tare da kananan 'ya'yanta domin su yi barar abinci sakamakon yadda mijinta ya ki ba su abinci. Hafsat ta ce, wani lokacin ma, ita ce take ciyar da mijin wanda ke kwance a gida cikin koshin lafiya.