Labaran RFI Hausa na karfe 5 cikin bidiyo 20/12/2023
Wallafawa ranar:
A cikin labaran na yau za ku ji yadda aka samu karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, yayinda a Jamhuriyar Nijar ake fama da kamfar magungunan asibiti. Sai kuma yadda zaben Congo ke ci gaba da gudana wanda 'yan takara 26 ke fafatawa. Akwai kuma hukuncin kotun Amurka da ya hana tsohon shugaban kasar Donald Trump damar tsayawa takara. Muna kuma tafe da rahotanni da hirarraki a cikin labaran.