Labaran RFI Hausa na karfe 5 cikin bidiyo 22/12/2023
Wallafawa ranar:
Faransa ta rufe ofishin jakadancinta da ke Jamhuriyar Nijar a yayin da rukunin karshe na sojojin kasar ya kammala ficewa daga kasar wadda ta fada hannun sojojin da suka yi juyin mulki. A Najeriya a na ci gaba da fama da karancin takardun naira a daidai lokacin da ake shirin gudanar da bukukuwan karshen shekara. Sama da mutane miliyan 7 sun tsere daga Sudan sakamakon yadda yaki ya mamaye wuraren da suke samun mafaka. Akwai rahotanni da hirarraki a cikin shirin.