Shekaru 10: Yadda birnin Lagos ke jimamin sace ƴan matan Chibok
Wallafawa ranar:
Yau ne aka cika shekaru 10 cur da mayakan Boko Haram suka sace ƴan matan Chibok da ke jihar Borno a Najeriya, lamarin da ya haddasa cece-kuce a kasashen duniya, yayin da har yanzu da dama daga cikin ƴan matan ke ci gaba da kasancewa a hannun mayakan ba tare da sanin makomarsu. Birnin Lagos na kan gaba wajen fafutukar ganin an ceto wadannan mata dalibai.