Latin-Amurka
Mutane 146 sun hallaka yayin karfarfar iska Hade da ruwan sama
Musu aikin ceto sun tabbatar da cewa akalla mutane 146 sun hallaka, yayin da karfarfar iska dake dauke da ruwan sama ta ratsa kasashen Latin Amurka.Irin wannan iska ita ce ta farko cikin shekara ta 2010 da ta ratsa kasashen, kuma ta’adin ya fi yawa cikin kasashen Guatemala da El Salvador da kuma Honduras.Masu aikin ceto sun kwashe tsawon sa’o’i wajen neman masu sauran nunfashi, a cikin kauyuka da rusassun gine gine.Akalla mutane 123 suka hallaka a kasar Guatemala, 59 suka bace. Mutane 14 suka hallaka a kasar Honduras, yayin wasu tara suka hallaka a kasar El Salvador.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: