Isa ga babban shafi
Russia-Belarus

Shugaba Lukashenko ya bada umurnin katse bututun gas

SHUGABAN Kasar Belarus, Alexander Lukashenko, ya bada umurnin katse iskar gas da Russia ke turawa kasashen Turai, bayan kanfanin Gazprom ya rage gas din day a ke baiwa kasar da kashi 30.Yayin ganawa da ministan harkokin wajen Russia, da aka nuna ta kafar talabijin, shugaban yayi gargadin cewar matsala tsakanin kasashen biyu, na iya komawa yakin gas, inda yake cewa, ba zasu lamince da kunyata su ba.Kasar Russia na zargin Belarus da kin biyan bashi Dala miliyan 200, yayin da Belarus ke zargin Russia da kin biyan bashin sama da Dala miliyan 200 da suke bin kanfanin Gazprom, na iskar gaz da yake turawa ta cikin kasar ta. 

(REUTERS)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.