MEXICO
Jami’an tsaron Mexico sun kashe Ignacio Coronel; kasurgumin mai fataucin kwayoyi
Jami’an tsaron Mexico sun hallaka Ignacio Coronel; wani kasurgumin mai fataucin kwayoyi a kasar.Shi dai Ignacio an tabbatar da cewa yana daga cikin mukarraban Joaquin Guzman da aka fi nema ruwa a jallo.Coronel wanda ya hallaka a lokacin musayar wuta da jami’an tsaro ana yi masa lakani da Sarkin Crystal, bisa yadda yake nuna kabura a hanyoyin fataucin miyagun kwayoyi zuwa Amurka.Shugaban kasar Mexico Felipe Calderon ya daura damarar yaki da masu fataucin kwayoyi da suka mayar da kasar zangonsu na ketarawa zuwa Amurka.
Wallafawa ranar: