Isa ga babban shafi
China

Furucin Clinton kan batun tsibiran Senkakus ya bata wa China rai

Yau juma’a kasar China ta nuna matukar bacin ranta dangane da furucin sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, cewa tsibiran Senkakus da ake takaddama a kansu, sun fada cikin da’irar kawancen tsaro ta Amurka da Japan.‘China na bayyana muguwar damuwa da matukar rashin jin dadi da wannan furuci da sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta yi a kwanan nan’, inji mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, cikin wata sanarwa a shafin yanar gizo.Ya ce ‘gwamnatin kasar Sin da al’umarta ba zasu taba amincewa da duk wani abu da ya shafi sanya tsibiran Senkakus karkashin yarjejeniyar hadin kai da tsaro ta kasashen Amurka da Japan ba’.  

Wani bangare na Tsibiran Senkakus dake gabashin tekun China
Wani bangare na Tsibiran Senkakus dake gabashin tekun China Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.