Isa ga babban shafi
Haiti

Rikici ya barke a Haiti bayan da kwalera ta kashe mutane 1,000

Wani rikici ya barke a kasar Haiti tsakanin Jami’an kiwon lafiya na Majalisar Dunkin Duniya da wasu ‘yan kasar inda jami’an kiyon lafiyar biyu suka mutu kan barkewar cutar kwalera a kasar da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu daya.Rikicin dai ya barke ne a tsakiyar birnin Hinche inda gungun wasu ‘yan kasar suka zargi jami’an kiwon lafiyar a matsayin wadanda suka yi haddasa barkewar cutar a kasar.Jami’an tsaro a kasar sun bayyana cewa mutane da dama ne ke kwance a gadon asibiti saboda rauni da suka samu sanadiyar rikicin.Jami’an kiwon lafiyar sun bayyana cewa wasu ‘yan siyasar kasar ne suka haddasa rikicin don samun shiga a zaben kasar da ke karatowa. 

wadanda ke fama da cutar kwalera a Asibitin Port Prince na kasar Haiti
wadanda ke fama da cutar kwalera a Asibitin Port Prince na kasar Haiti REUTERS/St-Felix Evens
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.