Isa ga babban shafi
VATICAN

Shugabannin kiristoci zasu gana kan cin zarafin kananan yara

A ranar Juma’a mai zauwa ne manyan shuwagabannin kristocin cocin Katolika zasu gana a birnin Vatican don tattauna batun cin zarafin kananan yara da malaman coci ke yi na luwadi dasu.Shugaba fafaroma Benedict ne ya bada sanarwar wanda kuma zai jagoranci taron tattaunawar.Wannan dai shi ne karo na farko da za’a gudanar da irin wannan taron na shuwagabbin kiristoci guda 203 a duniya da ke taka muhimmiyar rawa wajen zaben fafaroma shugaban Cocin katolika.A shekarar bara ne aka wallafa wani rehoto a kasar Ireland wanda ya fitar da dururuwan bayanan da suka shafi luwadi da malaman Coci ke yi da kananan yara. Rehoton wanda ya nuna cewa an fi samun haka a kasashen Amurka da kasashen Turai da suka da Jamus cibiyar Fafaroma.Taron wanda za’a gudanar zai fi maida hankali ne wajen tattauna al’amarin da ya faru a wata Coci a Ingila wacce ta amince da auren maza da kuma amincewa da mace a matsayin shugaban Coci. 

Fafaroma Benedict yana gaisawa da Antonios Naguib,Shugaban Cocin katolika ta Alexandria dake kasar masar
Fafaroma Benedict yana gaisawa da Antonios Naguib,Shugaban Cocin katolika ta Alexandria dake kasar masar Reuters/Osservatore Romano
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.