Isa ga babban shafi
Wikileaks

Wikileaks ya sake bankado wani sirrin Amurka

Shafin yanar gizon Wikileaks ya sake bankado wasu bayanan sirrin Amurka masu matukar muhimmaci ga sha’anin tsaron kasar da kan iya zama matsala yayin shirya kai wa kasar hari.Wadannan bayanan da shafin ya fitar su ne dai bayanai mafi muni da ke kokarin kunyata kasar Amurka da muzanta ta a idon duniya.Daga cikin bayanan dai akwai bayanin da suka bayyana tsohon shugaban kasar Australiya Kevin Rudd inda yake gargadin Sakatariyar harakokin wajen Amurka hillary Clinton kan daukar mataki akan kasar China idan har aka samu baraka da kasar.Wani bayanin da wikileaks ya bankado shi ne kan sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton wacce ta bayyana cewa kasar Saudi Arebiya ce kan gaba wajen taimakawa kungiyoyin Al ka’ida da Taliban da kuma kungiyar Hamas.A wani bayannin kuma Wikileaks ya bankado cewa jekadan Amurka a kasar Qatar yana cewa Qatar na amfani da kamfanin yada labaran Al jazeera a matsayin wata hanya mafi sauki wajen kulla yarjejeniya da sauran kasashen duniya.A watan Fabrairun bara ne dai Amurka ta aike da sako ga jami'an ta da ke kasashen waje, inda ta umarce su da su zayyana mata sunayen duk wadansu abubuwa da kan iya shafar lafiyar al'ummar ta ko tattalin arzikin ta, ko harkar tsaron cikin gida na Amurka.Akwai dai bayanai da suka shafi sauran kasashen turai musamman bayanai kan harakar sadarwa da sauran al’amurran da suka shafi yadda kamfanoni na kasashen Birtaniya da New Zealand suke gudanar da ayyukansu a Africa da yankin gabar ta tsakiya da kuma china. 

shafin yanar gizon Wikileaks,
shafin yanar gizon Wikileaks, ©Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.