Isa ga babban shafi
Palasdinawa-Isra’ila

Shugabannin Palesdinawa sun yi watsi da zargin da tashar Al-Jazeera ta watsa

Manyan Jami’an kungiyar Palasdinu, na tuhumar sahihancin bayanan asirin da tashar talabijin ta Aljazeera ta buga, wanda ya zargi shugabanin da tayin baiwa Isra’ila mafi yawa daga Yankin Birnin Kudus, dan sasanta rikicin dake tsakaninsu.Bayanan da tashar Aljazeera ta samu, mai dauke da shafuna 16,076, sun kunshi tarurrukan da bangarorin suka yi a tsakaninsu, sakonnin ta yanar gizo, tattaunawa tsakanin Palasdinu, Isra’ila da shugabannin Amurka, daga shekara ta 2000 zuwa 2010.Rahotan ya kara da cewa, shugabannin Palasdinawan sun yi tayin baiwa kasashen duniya, guraben ibada masu tsarki dake Birnin Kudus, da kuma rage adadin 'yan gudun hijira da zasu koma gida zuwa 100,000 a cikin shekaru 10.Tuni kungiyar Hamas ta bayyana shugabannin Palasdinawan a matsayin marasa gaskiya, kamar yadda Osama Hamdaz, kakakin kungiyar ya bayyana.Hamdaz ya kara da cewa, “Mu mun san wadannan shugabanin basu da gaskiya, kuma basu da hurumin tattaunawa a matsayin Palasdinawa, kuma wadanan bayanai sun tabbatar da zargin da muke yi.Babban mai shiga tsakani na kungiyar Palasdinu, Saeb Erakat, ya bayyana rahotan a matsayi wani shirin siyasa na bata musu suna.Erakat ya cigaba da cewa, “A shirye nake in nuna daukacin takardun tattaunawar da muke yi ga kowanne balarabe, wannan wani shiri ne na batawa shugaba Mahmud Abbas da kungiyar Plasdinu suna.”Tuni ake ci gaba da samun martani kan wannan rohoto da tashar Al-Jazeera ta fitar. 

Shugabannin Amurka, Isra'ila da Palesdinawa
Shugabannin Amurka, Isra'ila da Palesdinawa رویترز
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.