Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta yi kira ga kafa sabuwar gwamnati a Masar

Wata sanarwa da ta fito daga fadar White house ta Amurka, Gwamnatin kasar ta yi kira da a kafa sabuwar gwamnati a kasar Masar, kodayake a sanarwar babu wani kira dake nuna cewa shugaban kasar Hosni Mubarak ya yi murabus bayan shiga kwanaki bakwai na gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa. Rehotanni daga Amurka na nuna cewa Shugaba Barrack Obama ya nemi shugabannin yankin kasashen larabawa da su shiga tsakani wajen kawo karshen rikicin kasar. Tuni dai shugaban kasar Masar Husni Mubarak ya nemi goyon bayan rundunar sojin kasar bayan nada wani commandan Soji Omar Sulaiman a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da nada sabon Firimiya don kokarin magance zanga-zangar al’ummar kasar da ke kishirwar sauyin gwamnati. Sai dai kuma Hillari Clinton ta nemi shugaban ya kara yin tunanin abinda ya dace da talakawan kasar.Sanarwar ta Fadar White house na nuna cewa shugaba Obama ya bukaci shugabannin kasashen Isra’ila da Saudi Arebiya da kasar Turkiya ta wayar salula don tattauna rikicin kasar Masar tare da neman shawararsu kan yadda zasu magance rikicin .A yanzu haka dai an gargadi al’ummar kasashen duniya kan kaurace kai ziyara kasar Masar, inda wasu kasashe da suka hada da kasar Amurka da Iraq suka fara ceto ‘yan kasarsu mazauna Masar. Kasashen Turkiya da Indiya da Girka da Saudi Arebiya a yanzu haka sun tura jirage domin fara jigilar al’ummar kasarsu. 

wata mata mai suna Hu Yi Xin a filin saukar jiragen Pudon a Shanghai bayan sauka daga kasar Masar
wata mata mai suna Hu Yi Xin a filin saukar jiragen Pudon a Shanghai bayan sauka daga kasar Masar Reuters / Carlos Barria
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.