Isa ga babban shafi
Hukumar kula da Abinci ta Duniya

Za a Samu Habakar Noman Alkama a shekara ta 2011

A cikin wani hasashe da hukumar Noma da abinci ta MDD FAO ta fitar a yau Laraba, ya nuna cewa, a wannan shekara ta 2011 noma alkama a duniya zai karu, kamar yadda ita ma safarar cimakar zai karu a kasashen duniya 'yan rabbana ka wadatamu, sanadiyar tallafin da aka baiwa farashin.Hasashen farko da hukumar ta FAO ta fitar, ya nuna cewa a wannan shekara ta 2011 yawan noman alkamar a duniya zai kai ton miliyan 676, wanda hakan ke nuna samun karin kashi 3,4% akan na 2010 da ta gabata, kamar yadda rahoton hukumar ta FAO na wata uku uku, da ta fita a yau Laraba a birnin Rome na kasar Italiya ya nunar. 

Mike Goldwater/Getty Images
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.