Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya dauki matakin haraji domin rage kashe kudade

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya bukaci kara yawan harajin masu hannu da shuni, da kuma rage kashe kudaden Gwamnati, dan magance matsalar gibin kasafin kudin da kasar ke fama da shi.A lokacin da Mista Obama ya ke jawabi a Washington, shugaban yace “dole mu rage gibin kasafin kudin mu, ya kuma zama wajibi mu dauki tafarkin biyan basusukan da ake binmu, amma za muyi haka ne ta hanyar kare farfadowar da arzikin kasar yayi, kare masana’antu da kuma samar da aiyukan yi”.Sai dai kuma ‘yan jam’iyyar Adawa ta Republican tana ganin ba wannan bane matakin da ya dace da kasar Amurka, kamar yadda Senata McConnell jigo a jam’iyyar ya yi gargadin cewa kasashen duniya yanzu sun saka wa Amurka ido su gani domin yana shakkun Amurka zata fada cikin matsala kamar kasar Girka. 

Shugaban kasar Amurka Barrack Obama.
Shugaban kasar Amurka Barrack Obama. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.