Isa ga babban shafi
Bankin Duniya

Bankin Duniya zai taimaka wajen girka demokaradiya

Bankin Duniya ya ce zai maida hankali ne wajen taimakawa kasahsen da suka rungumi demokradiya sau da kafa.Shugbaan Bankin na Duniya Robert Zoellick ya bayyana cewa, idan aka duba yadda matashi ya jagoranci kawo juyin juya halin Tuniya bayan cinna wa kansa wuta.Ya yi alkawarin bankin zai taimaka wa kasar ta Tunisiya ta inganta ginshikan demokaradiya, tare da sauran kasashe musamman na Larabawa.Ya kara da cewa babu yadda bankin zai cimma burin da ake bukata ba tare da taimaka wa kasashe samun gwamnatoci na gari ba.Zoellick yace maganar ta yi kama da ta siyasa, amma tattalin arziki ne. Kasar Faransa dake shugabancin kungiyar kasashe masu bunkasan tattalin arziki na G20 ta goyi bayan shirin.Sakataren kudin Amurka Timothy Geithner ya ce cangi na hakika ke faruwa cikin kasashen Larabwa. Yayin da wasu kasashe masu tasowa suka lale marhaba da shiorin, kasashen Rasha da Saudiya sun nuna bakin ciki, tare da cewa bai dace Bankin na Duna ya tsunduma kansa cikin siyasa ba. 

Robert Zoellick shugaban Bankin Duniya
Robert Zoellick shugaban Bankin Duniya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.