Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mutane 12 sun hallaka a zanga zangar kasar Afghanistan

Akalla mutane 12 sun hallaka cikin wata zanga zangar da aka gudanar a yankin Arewacin kasar Afghanistan.Artabun da jami’an tsaro a garin Taloqan ya kuma janyo mutane 80 sun jikata, kamar yadda majiyoyin asibiti suka tabbatar.Kimanin mutane 2,000 sun shiga zanga zangar domin nuna adawa da harin da dakarun tsaron NATO ko OTAN suka kai, wanda ya yi sanadiyar hallaka mutane hudu da suka hada da mata biyu. Masu macin sun kuma wawushe kayan shaguna.Hallaka fararen hula cikin harin dakarun na NATO ke haifar da fushi na zaman dakarun tsakanin al’umar kasar. 

REUTERS/Omar Sobhani
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.