Isa ga babban shafi
Amurka

Yan majalasar kasar Amurika sun shigar da kara kan Shugaban kasar.

Yan majalasar kasar Amurika sun shigar da kara kan Shugaban kasar. Wasu ‘yan Majalisun kasar Amurka guda goma, sun shigar da kara kan shugaban kasar Barack Obama a gaban kotu, inda suke zargin shi da kai dakarun kasar a Libiya, ba tare da amincewar Majalisar ba.Yan Majalisun sun ce, matakin da shugaban ya doka ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar ta Amurika, wanda ya ce, duk wani yunkurin kai sojoji waje na sama da kwanaki 60, sai ya samu amincewar Majalisa.A martanin da ya mayar, shugaba Obama ya ce, ba sai ya nemi izinin Majalisa ba, kafin dakarun kasar, su cigaba da taimakawa rundunar tsaro ta NATO a Libiya, domin tsarin mulki ya bashi wannan damar, a matsayin shi na shugaban kasa. 

Babban magatakardan rundunar tsaro ta NATO  Anders Fogh Rasmussen
Babban magatakardan rundunar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen REUTERS/Francois Lenoir
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.