Turai
Kasashen Turai za su taimaki Girka
Shugabannin kasashe masu amfani da kudaden Euro yau sun sake wani yunkurin tallafawa matsalar tattalin arzikin kasar Girka, inda suka tsaida shawaran cewa cikin watan gobe ne zasu yanke irin sabon gudunmawar da zasu bayar.Da yake Magana bayan taron Ministocin kasashen dake amfani da kudaden Euro, su 17, mai Magana da yawunsu, Jean-Claude Junker ya fadi cewa sun jinkirta sai watan gobe batun gudunmawar kudin taimakon daya kai Euro, biliyan takwas.
Wallafawa ranar: