Isa ga babban shafi
MDD

Farashin abinci zai tashi a shekaru masu zuwa

Hukumar kula da noma da kuma Samar da abinci ta Majalisar Dunkin Duniya, ta yi gargadin samun hauhawan farashin kayan abinci, wanda zai jefa marasa karfi da kananan manoma cikin wani hali.Rahotan Hukumar, yace farashin abinci a bana, zai jefa masu karamin karfi da kananan manoma cikin mawuyacin hali, saboda hauhawan farashi, da kuma karancin kudaden shiga da marassa karfi ke fuskanta.Hukumar tace, yayin da manyan kasashe ke iya magance matsalar, ta hanyar kasuwanci, kananan kasashe, da kuma masu dogara da sayen abinci daga waje, musamman a Nahiyar Afrika, zasu fuskanci matsaloli.Rahoton yace, irin wannan hali kan tilastawa marassa karfi, su sayar da kadarorinsu da kuma bisashensu cikin rahusa, don samun abinda zasu ci.Hukumar ta bukaci Gwamnatoci da su kara mayar da hankali wajen kula da harkar noma, da kuma tallafawa kananan manoman wajen samun kasuwa, da kuma ingantaccen farashi. 

kayan Abinci da kayan Lambu a kasar China
kayan Abinci da kayan Lambu a kasar China 照片来源:路透社REUTERS/Stringer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.