Isa ga babban shafi
Faransa-Afganistan

Dakarun faransa 200 zasu fice daga Afganistan

A yau Laraba ne Karon farko na dakarun Faransa 200 zasu fice daga kasar Afganistan, bisa Alkawalin da Shugaba Nicolas Sarkozy ya yi a watan Yuni na janye Dakarun kasar daga Afaganistan. Kafin bukin Kirsimeti Faransa zata janye wasu dakarunta 200, tare da janye wasu dakarun 600 a farkon shekarar 2012 bisa yarjejeniyar kungiyar kawancen NATO na ficewa daga Afganistan kafin shekarar 2014.Dakarun NATO/OTAN kusan 130,000 ne ke gudanar da yaki a Afganistan amma kusan rabinsu Amurkawa ne, Faransa tana da yawan dakaru ne kusan 4,000 a Afganistan, da ke aikin tsaro yawancinsu a yankin Surobi da yankin Kapisa.Wannan ficewar na zuwa ne domin hannunta lamurran tsaro ga gwamnatin Afganistan kafin karshen shekarar 2014.Kasashen Amurka da Birtaniya da Belgium dukkaninsu sun bayyana fara ficewa da dakarunsu nan da watanni masu zuwa. 

Dakarun NATO/OTAN a’Afghanistan
Dakarun NATO/OTAN a’Afghanistan REUTERS/Baz Ratner
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.