Isa ga babban shafi
NATO/OTAN

NATO tace ta kashe ‘Yan Taliban 200 a Afganistan

Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO/OTAN, ta sanar da kamawa da kuma kashe ‘Yan kungiyar Taliban, dake da nasaba da kungiyar Haqqani a kasar Afghanistan.Kakakin kungiyar kawancen Tsaro ta NATO a kasar Afghanistan, Birgediya Janar Carsten Jacobson ne ya sanar da haka, bayan kaddamar da wani hari da ya kunshi daruruwan sojin Afghanistan, da ke samun taimakon dakarun NATO da ke yaki kan iyaka da kasar Pakistan.Janar Jacobson yace sun kawo karshen harin, wanda aka kaddamar da shi akan kungiyar Haqqani, da dakarun Afghanistan suka jagoranta kuma sun samun gagarumar nasara.Kakakin yace, sun kashe wasu ‘Yan Tawayen wadanda basu da alaka da kungiyar, cikin mako guda da suka kwashe suna dauki ba dadi.Kasar Amurka ta dade tana bukatar Pakistan ta dauki mataki kan kungiyar, kuma ko a makon jiya, Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta sanar da cewa sun fara tuntubar kungiyar. 

Wani jirgin yaki mai saukar Angulu a kan iyakar Afganistan da Pakistan
Wani jirgin yaki mai saukar Angulu a kan iyakar Afganistan da Pakistan REUTERS/Nikola Solic
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.