Isa ga babban shafi
Duniya

Martanin shugabannin duniya kan nasarar tattalin arzikin Turai

Hukumomin kasashen Duniya na ci gaba da mayar da martani kan yarjejeniyar da shugabanin kasashen Turai suka dauka, na magance matsalar tattalin arzikin da ya addabi wasu kasahsensu.Shugaban Bankin Duniya, Robert Zoellick, ya bayyana nasarar da shugabanin suka samu a matsayin matakin farko wajen magance matsalar, inda ya bayyana fatar ganin an kawo karshen ta da wuri, saboda kar ta yadu zuwa sauran kasashen duniya.Shugabar hukumar bada lamuni ta duniya, Christine Lagarde, ta yaba da ci gaban da shugabanin suka samu, wanda ta bayyana shi a matsayin takun farko.Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel tace sun yi nasarar cim ma muradun jama’a, kuma sun yi abin da ya dace, yayin da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy yace, sun dauki matakan duniya, mai cike da fata da kuma inganci, wajen shawo kan matsalar.Prime Ministan Britaniya, David Cameron yace an samu nasara wajen amincewa da shirin kara jarin Bankuna, wanda da aka nemi kaucewa.Shugaban Bankin kasashen Turai, Jean Claude Trichet, yace sun dauki duk matakan da ya dace ace sun dauka a matsayinsu na shugabani, yayin da Prime Ministan Girka, George Papendreou da kasarsa ta fi kowace fama da matsalar, ya bayyana ci gaban da aka samu a matsayin wani sabon babi, wanda ke bukatar Karin aiki.Tuni dai kasar China tace zata saye basukan kasashen Turai, matsayin da ya dada karfafa kasuwanni da darajar hannayen jari.Cim ma yarjejeniyar shugabanin ya sanya darajar kudin Euro tashi, yayin da hannayen jarin kasashen Turai suka cira sama.  

Ministocin kula kudin kasashen Turai
Ministocin kula kudin kasashen Turai REUTERS/Thierry Roge
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.