Isa ga babban shafi
G20-Greece

‘Yan adawa a Girka sun nemi Papandreou ya yi murabus

‘Yan adawa a kasar Girka sun bukaci Fira Minista George Papandreou ya yi murabus bisa matsalar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi inda suka nemi kafa gwamnatin hadin gwiwa inda Madugun adawa Antonis Samaras ya yi kiran gudanar da zabe cikin gaggawa.Yanzu haka George Papandreou ya janye matakinsa na gudanar zaben jin ra’ayin jama’a dangane da matakin tsuke bakin aljihu da kasashen Turai suka bukata domin ceto basukan da ke kan kasar.Papandreou ya fuskanci kalubalen ne tare da matsin lamba a Taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 da aka bude a birnin Cannes na kasar Faransa kan matakinsa na gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a.A yau juma’a ne kuma Majalisar kasar Girka zata kada kuri’ar amincewa da kudirin kasashen Turai, inda Papandreou ya nemi wakilan jam’iyyarsa ta gurguzu su bi hanyoyin da suka dace wajen ceto Girka daga matsalar da take ciki domin kaucewa ficewa daga kawance euro.Jam’iyyar Papandreou da ke da yawan ‘yan majalisu 152 cikin 300, wasu da dama cikin wakilan Jam’iyyarsa sun yi barazanar yin Tawaye ga kudirinsa. 

George Papandreou Fira ministan kasar Girka a taron kasashen G20
George Papandreou Fira ministan kasar Girka a taron kasashen G20 Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.