Kusan Mutane 70 sun mutu a hare haren kasar Iraqi
Wasu Jerin bama bamai sun tashi yau Alhamis cikin Bagadaza babban birnin kasar Iraqi, inda suka hallaka kusan mutane 70, abinda ya kawo adadin mutane da aka kashe zuwa kusan 300 a cikin makwanni biyu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An dai kai hare haren na yau ne a Sadr.
Rahotanni sun ce, harin na farko an kai shi ne a inda leburori ke jiran motar hawa, inda wani mai babur ya zo ya tada bam.
Hare haren kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin fahimtar juna tsakanin 'yan Shi'a da Sunnah, abinda ke barazana ga Gwamnatin hadin kan kasar.
Daga ranar 15 ga watan da ya gabata na Disamba, da aka samu hare haren da suka kashe mutane sama da 60 a cikin kasar, zuwa wanan rana, an samu munanan hare hare guda takwas, wadanda suka hallaka kusan mutane 300.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu