Isa ga babban shafi
Amurka

An Kammala zaben Jihar South Carolina na jam'iyyar Republican ta Amurka

Newt Gingrich ya lashe zaben Jihar South Carolina na tantance gwani karkashin tutar jam’iyyar adawa ta Republican ta kasar Amurka, inda ya doke babban abokin hamayyarsa Mitt Romney.

Newt Gingrich
Newt Gingrich © Reuters
Talla

Bayan kirga kusanin dukkanin kuri’un Mr Gingrich ya samu kashi 40 cikin 100, yayin da Mr Romney keda kashi 28 cikin 100. Duk wanda ya lashe jihar South Carolina ke samun nasara takara wa jam’iyyar tun shekarar 1980.

Rick Santorum na da kashi 18, sannan Ron Paul kashi 13. Duk wanda jam’iyyar ta Republican ta tsayar zai fafata da Shugaba Barack Obama na kasar ta Amurka yayin zaben kasa baki daya na watan Nowamba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.