Isa ga babban shafi
G20

Ministocin Kudin Kasashen G20 sun yi taro a kasar Mexico

Ministocin kudin kasashe mafiya samun bunkasan tattalin arziki na duniya, G20, suna taro kan magance matsalin tattalin arziki karo na biyu.Ana gudanar da taron na birnin Mexico City a kasar Mexico, da zumman samar da kudade da suka kai Dala tiriliyon biyu, domin magance matsalolin tattalin arziki da duniya ke fuskanta, wadda ke neman durkusar da tattalin arikin kasashen Turai.

REUTERS/Ariel Gutierrez/Presidential Palace/Handout
Talla

Taron ministocin kudin daga kasashe G20, ya zama mafi girma tun bayan na shekara ta 2008 da aka amince dad ala tiriliyon guda domin ceto matsalar tattalin arzikin da duniya ke fuskanta.

Wasu daga cikin kasashen sun koka da yadda ake neman tara kudade, amma basu da tacewa cikin hukumar bada lamuni ta duniya, IMF, inda kasashen na Turai da ake nema musu agaji keda tacewa ta karshe.

Anata bangaren kasar Jamus tace zai kai zuwa watan Mariskafin ta dauki mataki kan bada duk wani kudi domin tallafawa wata kasa daga nahiyar Turai dake cikin matsalar tattalin arziki.

Ministocin kasashen na G20 sun nuna yadda farashin man fetur ke ci gaba da zama barazana wajen magance matsalar tattalin arziki, inda ya zuwa Jumma’a ake sayar da gangan man kan $125, farashi mafi yawa cikin watanni 10. Saboda da sabani da Iran kan makamashin nukiyar kasar.

A wani labarin Wasu fitattun masana tattalin arzikin kasar Jamus, sun bayyana cewar, har yanzu kasashen Turai basu magance matsalar tattalin arzikin dake damun su ba.

Masanan da kan baiwa gwamnatin Jamus shawara lokaci zuwa lokaci, sun ce har yanzu akwai sauran rina a kaba, musamman hakar tafi da bankuna.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.