Amurka
Mitt Romney ya lashe zaben jam'iyyar Republican na jahar Illinois
Mitt Romney dan takarar da ke neman jam’iyar Republic ta kasar Amruka ta bashi damar tsayawa takarar neman kujerar shugabancin kasar, ya samu kashi 45% a jahar Illinois a gaban abokin takararsa Rick Santorum mai kashi 35%A cewar tashoshin TV na Fox News da CNN hasashe ya nuna cewa tsohon gwamnan Massachusetts arewa maso gabashin Amruka, ya samu ci gaba sosai a zaben fitar da dan takarar jam’iyar ta Republicain mai adawa a kasar ta Amruka, bayan da ya ke kan gaba a wasu jahohin da aka gudanar da zaben.
Wallafawa ranar: