Isa ga babban shafi
G8-Amurka

G8: Obama da Hollande zasu gana karon farko

Shugaban kasar Faransa François Hollande zai gana da shugaban kasar Amurka Barack Obama a karon farko kafin fara taron kasashe 8 masu karfin tattalin arzikin Duniya. Ana sa ran shugabannin biyu zasu tattauna batutuwan da suka shafi tsuke bakin aljihun gwamnati da ficewar dakarun NATO daga Afghanistan.

François Hollande Sabon shugaban kasar Faransa da Shugaban Amurka Barack Obama
François Hollande Sabon shugaban kasar Faransa da Shugaban Amurka Barack Obama RFi/Reuters
Talla

Shugaba Obama zai yi kokarin kulla sabuwar amintaka tsakanin shi da Hollande a Fadar White House kafin su kama hanyar zuwa taron G8 da matsalar tattalin arzikin Turai zai mamaye taron.

A makon nan ne aka rantsar da Hollande matsayin sabon shugaban kasar Faransa, kuma tun kafin rantsar da shi sabon shugaban ke kalubalantar matakin tsuke bakin aljihun gwamnati tare da bayyana kudirin shi na janye dakarun Faransa daga Afghanistan a karshen shekara.

Taron kasashen G8 dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da al’ummar Girka ke tsame kudadensu daga bankunan kasar bisa fargabar kasar na kama hanyar ficewa daga kungiyar kasashe masu amfani da kudaden euro.

Ana sa ran Dmitri Medvedev, ne zai wakilci shugaban Rasha Vladimir Putin wanda zai hadu da Hollande na Faransa da Mario Monti na Italia da Yoshihiko Noda na Japan da David Cameron na Birtaniya da Stephen Harper  da Markel ta Jamus da Obama na Amurka tare da kuma shugaban hukumar kasashen Turai Jose Manuel Barroso da Herman Van Rompuy wadanda zasu halarci taron.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.