Isa ga babban shafi
Tattalin Arziki

Prime Ministan Britaniya ya ce zai mara wa shirin shugaban Faransa Francois Hollande baya,

Shugabannin 2, da za su hadu a karon farko yayin taron shugabannin kasashen duniya masu yalwar tattalin arzikin kasa, da za a yi a Camp David na kasar Amurka, inda Mr Cameron zai nemi Sasanta wa da Hollade, bayan da ya ki sauraren shi lokacin yakin neman zaben shi.Ana sa ran shugaba Hollande dan gurguzu zai nemi a samar da tsare tsaren da za su samar da ci gaban kasashe. A lokacin taron na kungiyar G8. Yayin da Cameron mai ra’ayin mazan jiya yace gwamnatin kasar britaniya tana da ra’aayi irin na shugaban Faransa.Da alama suka da Mr Cameron ke ci gaba da sha a cikin gida saboda shirin shi na matse bakin aljihun gwmanti, ta sa shi ya fara kokarin tafiya tare da sauran shugabanin turai masu neman kawo ci gaba a baya bayan nan.Prime Ministan na Britaniya, ya kuma nemi kasashen na G8 su bayar da tallafi ga masu neman tabbatar da Democradiyya a kasashen larabawa. 

shuwagabanin kasashen gungun G8 a Washington.
shuwagabanin kasashen gungun G8 a Washington. REUTERS/Mike Theiler
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.