Za'a sake yin wani sabon zagayen tattauna shirin nukliyar kasar Iran
Kasar Iran da manyan kasashen duniya 6, sun amince su sake yin wani zagayen tattaunawa dangane da aikin nukiliyar Iran, wanda kasashen duniya ke zargin cewa na makamai ne, ba na samar da makamashi ba.
Wallafawa ranar:
Jakadiyar harakokin wajen Kungiyar tarayyar Turai Uwargida Cathrine Aston ce, ta bayyana haka, sai dai bata yi wani karin haske ba, dangane da yadda bangarorin 2 suka cimma wannan yarjejjeniya.
Sai dai kuma wasu majiyoyin sun bayyana cewa, manyan kasashen dunioyar guda 6 dake da ruwa da tsakki kan aikin nukiliyar kasar ta Iran wadanda suka hada da kasar Britania, China, Faransa, Russia, Amirka da kuma kasar Jamus za su ci gaba da zama tare da kasar ta Iran domin kara samun haske kan zargin da ake yi mata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu