Isa ga babban shafi
ICC-Afrika

Bensouda: Shugabar kotun Duniya ta farko daga Afrika

Da safiyar Jum’a ne aka rantsar da Fatou Bensouda ‘Yar kasar Gambia a matsayin babbar mai gabatar da kara a kotun hukunta laifukan Yaki ta ICC da ke birnin Hague. Bensouda ta karbi mukamin ne daga hannun Luis Moreno-Ocampo dan kasar Argentina wanda ya kwashe shekaru yana jagorancin Kotun.

Fatou Bensouda, sabuwar babbar mai gabatar da kara ta kotun Duniya
Fatou Bensouda, sabuwar babbar mai gabatar da kara ta kotun Duniya AFP / Daniels Evert -Jan
Talla

Besouda mai shekaru 51 na haihuwa ta kasance Mace ta farko da zata jagorancin Kotun, kuma shugaba ta farko daga Nahiyar Afrika.

Bensouda tana cikin alkalan da suka yi ruwa suka yi tsaki a binciken rikicin Rwanda da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

Sai dai an dade kasashen Afrika suna sukar kotun karkashin jagorancin Luis Moreno-Ocampo wanda ke shugabancin kotun tun a shekarar 2004.

Wasu ‘Yan Afrika dai suna ganin an kafa kotun ne domin cin zarafinsu.

Akwai jerin shugabannin kasashen Afrika da kotun k enema ruwa a Jallo da suka hada da shugaban Sudan Omar Hassan al Bashir da marigayi Kanal Gaddafi na Libya sai kuma tsohon shugaban Cote d’Ivore Laurent Gbagbo wanda ke jiran hukunci a Birnin Hague.

Amma a lokacin da Bensouda ke jawabi bayan rantsar da ita tace zata yi aiki domin kare Afrika.

An kwashe tsawon shekaru Takwas Bensouda tana matsayin mataimakiyar Luis Moreno-Ocampo al’amarin da yasa wasu suke kallon an bata mukamin ne domin yin amfani da ita wajen cin mutuncin ‘Yan Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.