Isa ga babban shafi
Turkiya-Syria-NATO/OTAN

Turkiya ta gargadi Syriya cewa zata mayar da martanin Soja idan Syriya ta yi kuskuren fada ikarta

Kasar Turkiya ta dauki alwashin maida martani a kan duk wani kuskuren keta haddin kan iyakarta da kasar Syriya zata yi nan gaba, kasar da a kullum ake ci gaba da tabka kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati da na yan tawaye a kewayen birnin Damas babban birnin kasar ta Syriya. A nata bangaren kungiyar tsaro ta Nato ko Otan, da a jiya litanin ta gudanar da wani zaman taron gaggawa a birnin Bruxelles na kasar Beljiyom bisa bukatar kasar Turkiya, bayan harbo jirgin saman yakinnta da kasar Syriya ta yi a ranar juma’ar da ta gabata, ta bayyana lamarin a matsayin abinda ba za a taba amincewa dashi ba, tare da nuna goyon bayanta ga kasar ta Turkiya. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.