Isa ga babban shafi
Amurka

Shugabannin Duniya sun taya Obama murnar lashe zaben Shugaban Amurka

Shugabannin kasashen Duniya sun taya Barack Obama murnar lashe zaben Shugaban kasa wa’adi na biyu bayan ya kada abokin karawar shi Mitt Romney na Jam’iyyar Republican. Kungiyar Tarayyar Turai da kasar China suna cikin wadanda ke sahun gaba wajen mika sakon taya murnarsu ga Shugaban.

Barack Obama tare da uwar gidansa  Michelle da mataimakinsa  Joe Biden suna murnar lashe zaben shugaban kasa karo na biyu a Chicago
Barack Obama tare da uwar gidansa Michelle da mataimakinsa Joe Biden suna murnar lashe zaben shugaban kasa karo na biyu a Chicago REUTERS
Talla

Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy, ya aiko da sakon shi ne ta hanyar shafin Twitter yana mai cewa “na ji dadin sake Zaben Barack Obama a matsayin shugaban kasa”

Jim kadan Bayan aiko da sakon Van Rompuy, shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya aiko da sakon taya Obama Murna daga kungiyar Tarayyar Turai. Tare da bayyana fatar ci gaba da aiki da Obama wajen kokarin warware matsalar tattalin arziki da tsaro da ke addabar kasashen Duniya.

A nasa bangaren Firaministan Birtaniya David Cameron yace yana fatar ci gaba da aiki da abokin shi Barack Obama bayan aiko da sakon taya murna ga nasarar da shugaban ya samu a shafin Twitter.

Shugaban Faransa Francois Hollande yace nasarar da Obama ya samu wata dama ce ta fito da hanyoyin samar da ci gaban tattalin arziki a kasashen Duniya.

Shugaban kasar China Hu Jintao ya mika sakon taya murnar shi ga Obama yana mai danganta ci gaban da kasashen biyu suka samu a shekaru hudu da Obama ya kwashe yana shugabancin Amurka.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya mika na shi sakon taya murna tare da kira ga Shugaba Barack Obama wajen ci gaba da taka rawa ga lamurran da suka shafi Afrika.

A na shi sakon taya murnar, Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki yace al’ummar kasar Kenya tushen Obama suna taya shi Murna tare da gudanar da gagarumin buki.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya mika na shi sakon taya murnar yana

mai cewa a zamanin mulkin Obama ne Isra’ila ta samu danganta mafi karfi tsakaninta da Amurka.

Natanyahu yace yana fatar ci gaba da aiki da Obama saboda ra’ayin da suke da shi wajen tabbatar da tsaro tsakanin Isra’ila da Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.