Isa ga babban shafi
Masar

‘Yan adawa sun yi kiran gudanar da zanga zanga a Masar

Kungiyoyin ‘Yan adawan a kasar Masar, sun yi kira da a fito a gudanar da zanga-zanga, domin nuna rashin amincewa da fadada ikonsa da Shugaban Kasar, Mohammed Morsi ya yi, inda suka ce ya wuce Gona -da –iri. “Wannan juyin mulki ne a kaikaice…saboda haka muna kira ga daukacin ‘Yan kasar Masar da su fito su nuna rashion amincewarsu a yau Juma’a.” Inji, Sameh Ashour, wani Lauya mai wakiltan kungiyoyin, a wani taron manema labarai. 

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi
Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi DR
Talla

‘Yan adawan haka zalika, sun zargi Morsi da mallake dukka bangarorin uku na kasar inda suka ce yana so ya mallake bangaren Shari’a.

A jiya Alhamis ne Shugaba Morsi ya ya bayyana wasu sabbin dokoki, inda ya nuna cewa, zai iya daukan duk wani mataki domin kaucewa juyin-juya hali.

Sanarwar da fadar shugaba Masar, ta kara da cewa wannan mataki da aka dauka ba za a iya kalubalantarsu ba kuma baza a iya daukaka kara ba.

Kwana daya ne dai rak daya jagoranci tsagaita wuta a yankin na Gaza, Shugaba Mohammed Morsi, ya gabatarwa mutan kasar sa jerin dokokin.

Yasser Ali, mai Magana da yawun Shugaban kasar ya fadawa gidatalabijin na kasar cewa Shugaban kasar zai kasance shi kadai keda ikon furta duk wata doka, na yadda yake son ayi, kuma babu wanda ya taka masa birki.

Wannan mataki dai bisa dukkan alamu, ba kamar cikas ya haifar bag a kungiyoyin kare democradiyya da suka kawar da mulkin tsohon Shugaba Hosni Mubarak bara.

Tuni dai Mohammed Albaradei tsohon Shugaban Hukumar kulada makamashin Nukiliya ta duniya, wanda dan kasar ne ya fito fili ya soki tsarin.

Shugaba Morsi har ila yau, yayi waje sauke Babban mai shigar da kara na gwamnati, Abdel Magreb Mahmud, inda ya nada Talat Ibrahim Abdullah.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.