Isa ga babban shafi
Amurka

Ranar da aka kashe ‘Yan makaranta a Connecticut ce ranar da hankali na ya fi tashi, inji Obama

Shugaban Amurka Barack Obama, ya ce kisan gillan da wani matashi ya yi wa yara ‘Yan makaranta Piramare, a jihar Connecticut ce ranar da ya fuskanci tashin hankalin da ya fi kowanne, tun da ya karbi madafun ikon kasar.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Obama ya kuma bayyana shakku kan bukatar da wasu masu neman a kyale masu so rike bindiga suka yi, na neman a samar da masu gadi, da za su rinka rike da bindiga a dukkan makarantun kasar, inda ya ce ba wannan ‘yan kasar ke son gani ba.
 

A ranar 14 ga wannan watan na Disamba, Adam Lanza, mai shekaru 20 ya hallaka mahaifiyar shi, kafin ya tafi wata makarantar elementary, ya kashe mutane 26, da suka hada da yara kanana 20.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.