Isa ga babban shafi
Mali-Faransa

Dakarun Faransa sun kai samame yankin ‘Yan tawayen Mali

Kasa da sa’oi 24 bayan ziyarar da Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, ya kai a kasar Mali, dakarun kasar Faransar, sun kai wani babban hari kan wani yankin 'Yan tawayen kasar dake kusa da garin Kidal, wanda gari ne da ‘Yan tawayen kasar ke rikeda shi a da. Rahotanni sun nuna cewa, akalla jiragen sama guda 30 ne suka kai samame yankin wanda ya hada da matsugunnan da ‘Yan tawayen ke shirya ayyukan hare-hare.  

Wasu yakin kasar Faransa a lokacin da suke kai samame a yankin 'Yan tawayen Mali
Wasu yakin kasar Faransa a lokacin da suke kai samame a yankin 'Yan tawayen Mali REUTERS
Talla

A dai ranar Larabar da ta gabata ne dakarun Faransa dake biye da dakarun Afrika suka karbe ikon filin saukan jiragen garin Kidal.

A ranar Asabar ne kuma Hollande ya kai ziyara kasar ta Mali inda dubbanin mutane suka tarbe shi suna nuna farin cikinsu, a yayin da aka bar wasu dakarun Faransa da na Chadi suna shawagi a Arewa maso Gabashin kasar.

Rahotannin na nuna cewa, dakarun na Faransa har ila yau basu samu cirjiya a wajen fafutukar da suke yi da ‘Yan tawayen na Mali ba wandanda ake ikrarin suna da alaka da kungiyar Al Qaeda.

Mafi aksarin ‘Yan tawayen kamar yadda bayanai ke nunawa, sun tsere zuwa cikin Hamada da tsaunukan dake kasar, inda anan ne ake kyautata zaton suka yi garkuwa da wasu Faransawa bakwai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.