Bakonmu a Yau
Bakonmu A yau: Dakta Aminu Umar, game da yarjenejiyar cinikin makamai ta duniya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:35
A karon farko Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da yarjejeniyar daidata cinikin makamai a duniya wanda kasashen Iran da Syria da kuma Korea ta Arewa ke adawa da shi.Kudirin ya samu amincewar kasashe 154 cikin 193 da ake da su a Majalisar. To amma wasu manyan kasashe wato Rasha da China sun kauracewa zaman majalisar.Dangane da haka ne Awwal Ahmad Janyau ya tattauna da Dakta Aminu Umar, wani kwararre kan siyasar kasa da kasa.