Isa ga babban shafi
China-Faransa

Gwamnatin China tace za ta saye jiragen Faransa 60

Gwamnatin China tace ta kulla yarjejeniya da gwamnatin Faransa game da kudirin sayen jiragen Airbus 60 a Faransa, a wata ziyarar da François Hollande ya kai a kasar domin inganta huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Ziyarar Hollanden Shugaban Faransa  a China
Ziyarar Hollanden Shugaban Faransa a China REUTERS/Mark Ralston/Pool
Talla

An kiyasta adadin kudin jiragen za su kai kudi Dalar Amurka biliyan bakwai da Miliyan Bakwai.

Kasashen China da Faransa sun cim ma wannan yarjejeniyar ne a ziyarar da shugaba François Hollande ya kai a Beijing.

Hollande wanda shi ne shugaban kasashen Yammaci na Farko da ya gana da sabon shugaban kasar China Xi Jinping, ya samu rakiyar attajiran kasar Faransa wadanda ke neman cin moriyar ci gaban tattalin arzikin kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.