Isa ga babban shafi
Koriya-Amurka

An yanke wa wani Ba’amurke daurin shekaru 15 a Koriya ta Arewa

Gwamnatin kasar Koriya ta Arewa tace ta yanke wa Kenneth Bae, hukuncin daurin shekaru 15 tare da yin aikin bauta a gidan yari. Kamfanin dillacin labaran Koriya na KCNA yace an yanke wa Pae Jun-ho da ake kira Kenneth Bae a Amurka, hukunci ne a ranar 30 ga watan Afrilu.

Kenneth Bae, Ba'amurken da aka yankewa hukucin daurin shekaru 15 a kasar Koriya ta Arewa
Kenneth Bae, Ba'amurken da aka yankewa hukucin daurin shekaru 15 a kasar Koriya ta Arewa REUTERS/Yonhap
Talla

A bara ne aka cafke Mista Bae bayan ya shiga yankin Koriya a matsayin dan yawon bude ido. Kuma Gwamnatin Koriya ta zarge shi da yunkurin kifar da gwamnatin kasar.

Wannan hukuncin na zuwa ne a dai dai lokacin da kasashen Amurka da Koriya ta Arewa ke adawa da juna bayan gwamnatin Pyongyang ta samu nasarar gwajin harba Makamin nukiliyarta karo na uku.

Kafofin yada labaran Koriya sun ce Mista Bae ya amsa tuhumar da ake ma sa.

A watan Nuwamban bara ne aka cafke Mista Bae a arewa maso gabacin birnin Rason da ke kusa da iyaka tsakanin Koriya da China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.