Isa ga babban shafi
Birtaniya

Kungiyar OIC ta yi tur da kisan Sojan Britaniya a London

Kungiyar kasashen Musulmi ta Duniya ta yi Tur, da kisan da aka yiwa wani Sojin kasar Britaniya a birnin London, da kuma nuna rashin jin dadi da yanda hukumomin kasar suka bayyana kisan da cewar mai alaka da Musulunci ne.A wata Takardar bayani mai Magana da Yawun kungiyar ya bayyana cewar kungiyar mai wakilai 57, ta nisanta kanta daga duk wani zargi na tada zaune tsaye, ko ayyukan Ta’addanci da ake alakantawa da Musulunci.Idan ana iya tunawa dai wasu mutane 2 ne aka ba da labarin cewar sun kai hari wa wani Sojin kasar Britaniya a London.Mutanen dai basu gudu ba, har aka zo aka harbe tareda jikkata su, a yayinda suka bayyana cewar sun yi hakan ne saboda Sojin kasar  na kisan Musulmi kullu yaumin.    

PM Britaniya David Cameron, yana bayyana kyamar kisan sojan kasar da aka yi
PM Britaniya David Cameron, yana bayyana kyamar kisan sojan kasar da aka yi REUTERS/Olivia Harris
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.