Isa ga babban shafi
Syria-Iran-Rasha

Babu batun sasantawa sai mayakan Hezbollah da Iran sun fice, inji ‘Yan tawayen Syria

Shugabannin ‘Yan tawayen Syria sun ce za su kauracewa taron sasantawa wanda kasar Rasha za ta jagoranta idan har Mayakan Hezbollah da Iran na taimakawa dakarun gwamnatin Bashar al-Assad. Duk da ‘Yan tawayen sun fuskanci baraka a tsakaninsu a taron Istanbul.

'Yan tawayen Syria
'Yan tawayen Syria Reuters
Talla

Shugaban ‘Yan tawayen na Syria George Sabra yace za su kauracewa duk wani taron sasantawa idan Gwamnatin Assad na samun taimako daga wasu dakarun kasashen waje.

An kwashe tsawon mako guda dakarun Assad tare da hadin gwiwar dakarun Hebollah suna yaki domin karbe ikon Qusayr da ke hannun ‘Yan tawaye.

Wannan kuma na zuwa ne bayan shugaba Bashar Assad ya fito ya bayyana samun taimakon manyan makamai daga kasar Rasha bayan kasashen Turai sun janye takunkumn makamai ga ‘Yan tawaye.

Wannan dai wani sabanin ra’ayi ne tsakanin Rasha da kasashen Turai game da rikicin Syria.

03:35

Dr. Uba Ahmed Jos

Kasar Amurka ta bukaci kungiyar Hezbollah ta gaggauta janye dakarunta daga kasar Syria.

Wannan gargadin ya zo ne a dai dai lokacin da Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ke cewa yanzu haka akwai dakarun kungiyar ta Hezbollah akalla dubu uku zuwa dubu hudu da suka shiga kasar Syria domin kare gwamnatin Assad.

Fabius, yace rawar da kungiyar ke takawa a rikicin Syria, abu ne da zai iya haifar da cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi wajen kawo karshensa.

A watan gobe ne kasahsen Duniya suka shirya gudanar da taro a Geneva domin tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin Syria, sai dai kuma Gwamnatin Iran da Rasha ke bukatar wakilcinta a taron, tace taron na shan shayi ne kawai da za’a yi a watse.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.