Isa ga babban shafi
Afghanistan

Kungiyar Taliban ta kai hari a tashar jirgin sama a Kabul

Kungiyar Taliban ta kai wasu jerin hare hare a tashar jirgin birnin Kabul a Afghanistan, kuma an ji karar harbin bindiga da fashewa a kusa da unguwar da mafi yawanci akwai sansanin Sojin kasashen waje.

Jami'an tsaron Afghanistan suna binciken harin da aka kai a tashar jirgin sama a Kabul
Jami'an tsaron Afghanistan suna binciken harin da aka kai a tashar jirgin sama a Kabul REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Kakakin gwamnatin Afghanistan Sediq Sediqqi yace maharan sun fake ne a wani gida da ke kusa da tashar jirgin a Kabul inda suka kwashe tsawon sa’o’I hudu suna musayar wuta da Jami’an tsaro.

Kungiyar Taliban ta yi ikirarin kai harin, inda nan take aka dakatar da tashi da saukar jirage tare da rufe hanyoyin zuwa tashar jirgin.

Wannan harin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar tsaro na NATO ke shirin mika ragamar tafiyar da tsaro ga Jami’an tsaron Afghanistan kafin karshen 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.