Isa ga babban shafi
Masar

An samu hasarar rayuka sakamakon zanga zangar da ake yi a Masar

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon mummunar zanga zangar da masu adawa da shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi suka yi, inda suka bukace shi da ya sauka daga mukamin sa nan da gobe Talata. 

Arangama tsakanin magoya bayan Shugaba Morsi da masu adawa a kasar Masar
Arangama tsakanin magoya bayan Shugaba Morsi da masu adawa a kasar Masar REUTERS/Stringer
Talla

Rahotanni har ila yau na nuna cewa wasu kuma da dama sun samu raunuka a arangamar.

Dubban mutane suka shiga zanga zangar a Dandalin Tahrir, da kuma wasu garuruwa da dama, yayin da suma masu goyan bayan shugaban suka gudanar da tasu zanga zangar.

Shugaba Morsi ya yi tayin tattaunawa da ‘yan adawar, amma kuma shugabaninsu sun yi watsi da tayin.

“Tattaunawa ita ce mafitar da za ta samar da zaman lafiya.” Inji mai magana da yawun shugaba Morsi, Ehab Fahmy.

“Gwamnati a shirye ta ke ta yi tattaunawa mai ma’ana.” Ya kara da cewa.

Sai dai masu adawa da gwamnatin ta Morsi sun ce, sam suna so ne kawai Morsi ya sauka inda aka jiyo suna raira wakokin nuna kyamar gwamnatin ta sa.

Wata majiyar soji ta bayyana cewa wanna gangami shine da ya fi samun halartar mutane da dama.

Tuni wani babban ‘yan adawa ya yi kira ga bangaren sojin kasar da su zauna cikin shiri domin karbar ragamar mulkin kasar.

A daya bangaren kuma, masu goyon bayan shugaban suma sun gudanar zanga zanga a ‘yan kwanakin nan domin kare gwamnatin ta Morsi.

Rahotanni na nuna cewa bankuna da shaguna sun kasance a rufe a jiya Lahadi duk da cewa rana ce ta aiki.

A jiya Lahadi ne gwamnatin ta Morsi ta cika shekara daya da fara tafiyar da harkokin kasar bayan Morsin ya lashe zabe a shekarar da ta gabata da yawan kuri’u miliyan 13.2.

Sai dai bangaren ‘yan adawan na ikrarin cewa a karshen makon da ya gabata sun tattara sunayen mutane miliyan 22 wadanda suka rattaba a hanu na neman Morsi ya sauka daga kan mulki a kuma gudanar da sabon zabe.

Morsi ya kasance shugaban Masar na farko da aka zaba ta hanyar daurarriyar demokradiya tun bayan tunbike gwamnatin Hosni Mubarak wanda ya kwashe shekaru da dama yana mallakar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.